<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>189</hymn_number>
<title>Dā, Ban San Labarin Yesu Ba LW189</title>
<lyrics>[V1]
 1) Dā, ban san labarin Yesu ba,
 Cikin duhu na bi hanyata,
 Ban ko kula akwai ceto ba
 Gun giciye.

[V2]
 KORUS
 Jinƙai marar iyaka ne fa.
 Gafara a yalwace ya yi,
 Har ya kau da dukan zunubi
 Kan giciye.

[V3]
 2) Da na ji labarin cetonsa,
 Na ji nauyin kayan laifina.
 Sai na tashi neman gafara
 Gun giciye.
 Korus

[V4]
 3) Duba yawan girman ƙaunarsa,
 Duba irin aikin gafara!
 Da jininsa ne ya fanshe mu
 Kan giciye.
 Korus

[V5]
 4) Daga nan na zama bawansa,
 Ya yarda ya zama Sarkina.
 Akwai murna cikin zuciyata
 Don giciye.
 Korus</lyrics>
</song>